in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta rattaba hannu kan yarjejeniya da Saliyo domin yaki da barkewar Ebola
2014-09-23 11:54:50 cri

Jakadan kasar Sin a Saliyo Zhao Yanbo ya kara jaddada sadaukarwar kasar Sin a kokarin da take yi na taimakawa Saliyo tunkarar kalubale na barkewar cutar Ebola, mai saurin kashe bil'adama.

Jakada Zhao Yanbo wanda ya bayyana hakan a yayin da yake rattaba hannu a kan sharuddan aiki da Saliyo, da kuma daukokin aiki na sabuwar tawagar masanan kiwon lafia daga kasar Sin.

Jakadan ya ce, tarihi ya nuna cewar, gwamnatin kasar Saliyo ta nuna gagarumar damuwa a lokacin da Sin ta yi fama da matsalar barkewar murar tsuntsaye, kuma wannan shi ya sa ita ma kasar Sin take tuna mutuntawar da Saliyo ta yi mata, tare da yanke shawarar daukar mataki na tallafawa Saliyo a yakin da take yi da barkewar cutar Ebola.

Jakadan ya ce, sun samar da kwararrru 29, masu gudanar da gwajin cututtuka, da kuma wasu kwararru 30, wadanda suka kware a fannin duba lafiyar majiyyata, kuma dukkansu sun isa kasar ta Saliyo ne daga cibiyar hana yaduwar cututtuka da rigakafi ta kasar Sin, to amma jakadan ya ce, wsu daga cikin kwararrunsu sun fito ne daga wasu manyan asibitoci na kasar Sin.

Ma'aikatar lafiya ta kasar Saliyo ta ce, gwamnatin kasar na sa ran karbar wadansu kayayyakin kula da lafiya da na kashe cututtuka wadanda ta yi oda daga kasashen ketare. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China