IMF na tunanin samar da kudi ga kasashe uku na yammacin Afirka don sassauta tasirin da cutar Ebola ta yi musu a fannin tattalin arziki
Jaridar Daily Observer ta kasar Liberia ta bayar da labari a ranar 24 ga watan nan cewa, asusun bada lamuni na duniya wato IMF ya bada shawara ga hukumar darectocin zartaswarsa da a kara samar da kudi dala miliyan 127 ga kasashen Liberia, Guinea da Saliyo, don taimakawa kasashen uku na yammacin Afirka wajen yaki da cutar Ebola,.
Labarin ya bayyana cewa, idan hukumar ta amince da wannan shawara, kudin da za a samar zai taimakawa kasashen uku sosai wajen yaki da cutar Ebola a watanni 6 zuwa 9 masu zuwa. (Zainab)