Kazalika, bayan ganawar, shugabannin biyu sun halarci bikin sa hannu kan yarjejeniyoyin hadin kai da suka shafi fannonin diplomasiyya, cinikayya, muhimman ababen more rayuwa da sauransu.
Ban da haka kuma, shugabannin biyu sun zanta da manema labaru, inda shugaba Xi ya jaddada cewa, kasashen biyu sun yanke shawarar kafa sabuwar dangantakar hadin kai a dukkan fannoni, abin da ya samar da makoma mai haske a hadin gwiwar da ke tsakaninsu tare da kara bunkasa dangantakar dake tsakaninsu. (Amina)