Yau Jumma'a 12 ga wata, a birnin Dushanbe, hedkwatar kasar Tajikistan ne aka yi taron kwamitin shugabannin kasashe mambobin kungiyar yin hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO karo na 14, inda shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya halarta tare da yin jawabi.
A cikin jawabinsa, shugaba Xi ya nuna cewa, tabbatar da ganin kungiyar SCO ta ci gaba da bin manufar bunkasuwa kamar yadda aka tsara a baya, a kokarin kara samarwa mambobin kungiyar da jama'arsu tsaro da alheri shi ne babban nauyin da aka dora wa dukkan mambobin kungiyar. Saboda haka Xi ya gabatar da ra'ayinsa a fannoni 4, da farko, ya zama dole ga mambobin kungiyar su nace ga sauke nauyin kiyaye kwanciyar hankali da tsaro a yankin da kungiyar SCO take. Na biyu dole ne a nace ga mayar da samun bunkasuwa da wadata tare a matsayin manufar dukkan mambobin kungiyar. Na uku, wajibi ne a nace ga kara azama kan samun fahimtar juna a tsakanin al'ummar yankin, tare da kara yin mu'amalar sada zumunci ta fuskar al'adu daga sassa daban daban. Na hudu kuwa, wajibi ne a nace ga habaka yin mu'amala da hadin gwiwa da kasashen ketare. Kungiyar tana maraba da dukkan kasashen da suke fata kuma suka cancanta da su zama mambar kungiyar a hukumance. Kasar Sin na maraba da mambobin kungiyar, kasashe masu sa ido, kasashen da ke hada kai da kungiyar da su shiga cikin ayyukan raya shiyyar raya tattalin arziki ta hanyar siliki, a kokarin kara azama kan hadewar yankin da raya yankin ta hanyar masana'antu ta sabon salo. (Tasallah)