Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, gabanin bude taron hadin gwiwa na Shanghai ko SCO karon na 14.
Yayin zantawar tasu, shugaba Xi ya bayyana gamsuwa da irin ci gaban da dangantakar kasashen biyu ke samu. Ya ce, shi da shugaba Putin sun cimma wasu yarjejeniyoyi a baya bayan nan a tattaunawar Shanghai da Fortaleza.
Kaza lika shugaban kasar ta Sin ya bayyana halartar kaddamar da shimfida bututun iskar gas da zai hada kasashen biyu da shugaba Putin ya yi, a matsayin wata manuniya dake fayyace himmarsa ga hadin gwiwar kasashen nasu.
Har wa yau Xi ya jaddada muhimmancin dake akwai na ci gaba da fadada hadin kai daga dukkanin fannoni. Tare da batun kammala aikin shinfida bututun iskar gas din da aka fara kan lokaci, baya ga daga matsayin hadin gwiwar sassan biyu ta fuskar makamashi.
Shi kuwa a nasa bangare, shugaba Putin na'am ya yi da matsayin dangantakar sassan biyu ta fuskar harkokin cinikayya da tattalin arziki, yana mai bayyana fatan dorewar huldar kasashen biyu a dukkanin sassa, musamman ma fagagen makamashi, da na sufurin jiragen sama, da cinikayya da kuma gine-ginen ababen more rayuwa.
Bugu da kari shugaba Putin ya jaddada aniyarsa ta ganin an gaggauta kammala aikin shimfida bututun iskar gas da zai hada kasashen biyu kan lokaci, saboda irin muhimmancin da aikin ke da shi. (Saminu)