Shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya gabatar a ranar Alhamis a Douchanbe da ra'ayin gina wani yankin kasuwanci da zai hada Sin, Mongoliya da Rasha.
Mista Xi ya gabatar da wannan ra'ayi ne a yayin wani zaman taro tare da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da shugaban kasar Mongoliya Tsakhiagiin Elbegdori a yayin dandalin kungiyar huldar dangantaka ta Shanghai (SCO) karo na 14. Ya jaddada cewa, dabarun cigaban kasashen uku dake makwabtaka da juna na da karfin tafiya yadda ya kamata, shugaba Xi ya nuna cewa, a lokaci guda Rasha da Mongoliya sun ba da amsa mai kyau kan tsinkayen kasar Sin na gina wani yankin kasuwanci a kan tsawon hanyar siliki.
Kasashen uku, in ji mista Xi, na iyar hada shirin yankin kasuwanci na hanyar siliki tare da shirin Rasha na gina layin dogon kasa da kasa, da shirin Mongoliya na hanyar ciyayi, da kuma aiki tare wajen gina wani yankin kasuwanci na Sin-Mongoliya-Rasha.
A cikin tsarin wannan shirin, mista Xi ya bayyana fatan ganin kasashen uku sun kara karfafa dangantakarsu a fannoni daban daban, kamar yawon bude ido, tawagogin tuntubar juna da nazari, sadarwa, kare muhalli, da ma rigakafi da aikin ba da agaji idan wani bala'i ya faru. Haka kuma ya kamata kasashen uku su kara karfafa huldarsu bisa tsarin SCO, da tabbatarwa juna tsaron shiyyar cikin hadin gwiwa, da kuma samun cigaba tare, in ji shugaban kasar Sin. (Maman Ada)