Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci kusoshin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da na gwamnati kasar da su daukaka aikin koyarwa, ta yadda zai zamanto aiki mafi girma a kasar Sin.
Xi ya bayyana hakan ne a yayin da ya kai ziyarar aiki a jami'ar horar da malamai ta Beijing, a jajibirin ranar malamai ta kasar Sin, kuma ya kara da cewar, inganta matsayin ilmi da arzikin kasa na bukatar malamai masu jini a jika, wadanda suka kware tare da sanin sharuddan ayyukansu.
Shugaban kasar ta Sin, ya yi kira a kan malamai da su daga tutar ilmin kasar Sin, tare da sadaukar da kansu wajen karbar sauye-sauye na zamani.
Xi, ya kuma bukaci dukanin matakai na gwamnatocin kasar Sin da su sanya ilmi a cikin jerin ajandarsu ta farko, tare da ci gaba da kokari wajen wanzar da canje-canje a bangaren ilmi.
A yayin wani zama da ya yi da malamai daga yankunan karkara, Xi, ya ce, akwai bukatar kara fafutukar bunkasa ilmi a yankunan yammacin kasar Sin, da kuma yankunan karkara da tsibirai dake lunguna. (Suwaiba)