in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya kammala ziyara a Tajikistan
2014-09-14 17:09:14 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kammala ziyarar aikin da ya gudanar a kasar Tajikistan, kana ya tashi daga birnin Dushanbe zuwa zango na gaba, wato kasar Maldives a safiyar Lahadin nan bisa agogon wurin.

Yayin ziyararsa a kasar Tajikistan, shugaba Xi ya halarci taro karo na 14, na hukumar kungiyar hadin gwiwa ta birnin Shanghai SCO, wanda ya gudana tsakanin ranekun 11 zuwa 12 ga watan nan, kana ya tattauna da shugaban kasar Tajikistan Emomali Rakhmon. Shugabannin 2 sun kuma ganewa idanunsu yadda aka fara aiki da wasu manyan ayyukan hadin gwiwar kasashen nasu.

Wannan ziyara dai ta kasance ta farko da shugaba Xi ya gudanar a kasar Tajikistan, kuma karo na biyu a tsakiyar Asiya, tun bayan kama ragamar mulkin kasar ta Sin. Kaza lika wannan ne karo na biyu da ya halarci taron koli na SCO.

Ana dai sa ran shugaban kasar ta Sin zai ziyarci kasashen kasar Maldives, Siri Lanka da kuma Indiya kafin dawowar sa gida. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China