in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping zai halarci taron shugabannin SCO
2014-09-11 10:56:07 cri
Da sanyin safiyar Alhamis din nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tashi zuwa birnin Dushanbe na kasar Tajikistan, domin halartar taro karo na 14 na shugabannin hukumar kungiyar hadin gwiwar Shanghai ta SCO.

Shugaba Xi wanda zai halarci taron bisa gayyatar da takwarorinsa na kasashen Tajikistan da Maldives da Sri Lanka da kuma India suka yi masa, zai kuma kai ziyarar aiki ga kasashen hudu.

Cikin tawagar 'yan rakiyarsa akwai uwargidan sa madam Peng Liyuan, da wakilin ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta Sin Wang Huning, da babban magatakardan sakatariyar kwamitin tsakiya Li Zhanshu, da wakilin majalisar gudanarwar kasar Yang Jiechi, da kuma sauran manyan kusoshin gwamnati. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China