Ranar 3 ga watan Satumbar nan rana ce ta cika shekaru 69, tun bayan da kasar Sin ta samu galaba kan hare-haren da sojojin kasar Japan suka kaddamar da yaki da amfani da karfin tuwo, kana rana ce da ta kasance ta farko, da zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta tsaida kuduri, na kafa ranar tunawa da cimma nasarar yaki da hare-haren da sojojin Japan suka kaddamar.
A wannan rana da safe shugaban kasar Sin Xi Jinping, da firaministan kasar Li Keqiang da sauran shugabannin kasar na jam'iyyar kwaminis ta kasar sun halarci babban dakin tunawa da yaki da hare-haren da sojojin Japan suka yi, inda aka jera furanni tare da wakilan bangarori daban daban na birnin Beijing, domin nuna alhinin rasuwar mutanen da harin na Japanawa ya rutsa da su.
A ranar 2 ga watan Satumbar shekarar 1945 ne dai gwamnatin kasar Japan, ta rattaba hannu kan takardar mika wuya, wanda hakan ke nuna cewa an cimma nasarar yakin da aka yi na nuna karfin tuwo na kasa da kasa. A kuma ranar 3 ga watan Satumbar wannan shekara ne aka gudanar da bikin murnar cimma wannan nasara a dukkan fadin kasar Sin.
Tun daga lokacin da aka fara wannan yaki da kasar Japan a ranar 18 ga watan Satumbar shekarar 1931, ya zuwa lokacin da sojojin Japan suka mika wuya a shekarar 1945, al'ummar kasar Sin ta yaki dakaru masu dauke da makamai har tsawon shekaru 14. Ya zuwa watan Febrairun bana, zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya tsaida wata doka, inda aka maida ranar 3 ga watan Satumba a matsayin ranar tunawa da yakin da aka yi da hare-haren dakarun sojin kasar ta Japan. (Zainab)