Jim kadan da fitar wannan sanarwa, wani binciken ra'ayin jama'a da aka gudanar ya shaida cewa kashi 80% na jama'ar kasar suna goyon bayan manufar shugaba Poroshenko game da wannan lamari. Koda yake shugaban na Ukraine ya ce majalisa ta yanzu za ta ci gaba da aikinta kafin kafuwar wadda za ta maye gurbinta.
Majalisar dokokin kasar mai ci dai ta fara aiki ne a shekarar 2012, yayin da tsohon shugaban kasar Viktor Yanukovych ke kan kujerar mulki, don haka wa'adin aikinta zai kai ga shekarar 2017, idan ba wani canji aka samu ba.
Sai dai bayan da Poroshenko ya dare karagar mulki a watan Mayun bana, ya alkawarta gudanar da zaben majalisar ta dokoki kafin karshen wannan shekara, ganin yadda a cewarsa majalisar ta yanzu ta gaza wakiltar moriyar al'ummar kasar, balle ma bukatarsu a fannin siyasa. (Bello Wang)