Ministan harkokin wajen Sin ya yi kira da a kiyaye zaman lafiyar yankin Gaza yadda ya kamata
Yayin da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ke ganawa da takwaransa na kasar Sudan Ali Ahmed Karti a birnin Beijing a yau Laraba 27 ga wata, Mr. Wang ya nuna matsayin kasar Sin kan yadda Falesdinu da Isra'ila suka kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta a yankin Gaza, inda ya bayyana cewa, kasar Sin tana maraba da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Falesdinu da Isra'ila suka kulla a tsakanisnu, ta kuma nuna yabo matuka ga kokarin da kasar Masar da bangarori daban daban da abin ya shafa suka yi kan wannan lamari, wannan ya kasance wani muhimmin mataki wajen sassauta tashin hankalin da ake fuskanta a yankin Gaza, da kuma kawar da kuncin da jama'ar yankin suke sha a halin yanzu. Haka kuma, kasar Sin na fatan Isra'ila da Falesdinu za su mai da hankali kan shimfida zaman lafiya mai dorewa a yankin Gaza, kiyaye zaman lafiyar jama'a, da kuma kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta din-din-din. Bayan haka kuma, ana fatan bangarorin biyu za su farfado da shawarwarin samar da zaman lafiya tsakaninsu cikin sauri, ta yadda za a warware matsalar Falesdinawa yadda ya kamata, da ciyar kokarin samar da dauwamammen zaman lafiya da tsaro a wannan yanki gaba.
Bugu da kari, Mr. Wang ya kara da cewa, kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan goyon bayan samar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falesdinu a ko da yaushe, haka kuma, za ta ci gaba da yin kokari wajen ganin an samar da zaman lafiya tsakanin Falesdinu da Isra'ila da kuma kiyaye zaman karko a yankin. (Maryam)