Qing Gang ya ce, kwanan baya, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya sake jaddada matsayin kasar Sin kan batun yankin Gaza, inda ya yi kira da a kawo karshen musayar wuta ba tare da bata lokaci ba don kiyaye tsaron jama'ar yankin.
Minista Wang zai tafi birnin Alkahira don karfafa aikin shimfida zaman lafiya a yankin zirin Gaza. Rikicin da jama'ar yankin Gaza suke fama da shi a halin yanzu ya tayar da hankulan jama'ar kasar sosai, shi ya sa, kasar Sin ta riga kuma take ci gaba da ba da taimako yadda ya kamata ga Falesdinu da yankin Gaza. Bugu da kari, kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa tare da gamayyar kasa da kasa wajen cimma burin tsagaita bude wuta a yankin Gaza da kuma kiyaye zaman lafiyar yankin. (Maryam)