Wata kafar talabejin ta kasar Masar ta rawaito Abbas na cewa babban dalilin wannan bukata ta komawa shawarwari shi ne, kaiwa ga dakatar da zub da jinin fararen hula.
Bangarorin Falasdinu da na Isra'ila dai sun yi watsi da 'yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma ta baya bayan nan ne a ranar Talatar da ta gabata, bayan dakatar da musayar wuta tsahon kwanaki 9.
A wani ci gaban kuma babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon ya bukaci Firaminstan Isra'ila Benjamin Netanyahu, da ya dauki matakan dakile ci gaba da kaddamar da hare-hare a Gaza, tare da rungumar kudurin kasar Masar na shiga tsakani.
Wata sanarwa da kakakin sa ya fitar, ta ce a jiya Asabar Mr. Ban ya zanta da Firaminista Netanyahu ta wayar tarho, a kokarinsa na habaka shawarwari tsakanin masu ruwa da tsaki kan rikicin da sassan biyu ke tsaka da fafatawa. (Saminu Alhassan)