A wata sabuwa kuma gidan rediyo na Isra'ila ya ruwaito wani rahoton majiyoyin 'yan sanda da sojojin Isra'ila wadanda ke cewa an harba wadansu rokoki biyu zuwa kudancin Isra'ila kafin karshen wannan yarjejeniyar tsagaita bude wutar, kuma duk da yake rokokin ba su lahanta kowa ba, amma babu wanda ya dauki alhakin kai harin.
Kakakin kungiyar Hamas Sami Abu Zuhri, ya bayyana a cikin wani sakon da aka aiko da shi ta kafar sadarwa ta i-mel, cewar kungiyarsa ba ta da hannu a harba wata roka cikin Isra'ila a safiyar Jumma'a ta yau.
Hakazalika wani jigo a kungiyar ta Hamas, Ismail Radwan ya bayyana a Gaza cewar, babu wata yarjejeniyar da aka cimmawa tsakaninsu da Isra'ila.
Shi ma wani mutum daga bangaren Isra'ila dake garin Bethlehem ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Maan cewar bangarorin biyu ba su daidaita a kan samar da tsagaita bude wuta ta din-din-din ba. (Suwaiba)