in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babu wata yarjejeniyar kara adadin tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas
2014-08-08 10:52:47 cri
Wani jami'in Isra'ila wanda ba'a bayyana sunansa ba ya shaidawa jaridar Ha'aretz cewar, kawo daren ranar Alhamis, babu wata yarjejeniyar kara tsawon yarjejeniyar tsagaita wutar ta jin kai ta awowi 72, wacce adadinta zai kare yau Jumma'a.

Hakazalika wasu jami'an tsaro sun shaidawa wani shafin labaran Intanet, da aka yi wa lakabi da walla, cewar firaminista Benjamin Netanyahu na kasar Isra'ila da kuma ministan tsaro na kasar Moshe Ya'alon sun bada umurni ga rundunar tsaro ta Isra'ila dake kudancin kasar da ta kasance a cikin shiri domin tunkarar yiwuwar komawa wuta daga zirin Gaza.

Shafin na Intanet na walla ya ruwaito cewar jami'an sun ce Isra'ila za ta maida martani mai karfi idan har aka ci gaba da kai hari daga zirin gaza zuwa cikin kasarta.

Tun farko, Isra'ila da Hamas sun amince da tsagaita bude wuta a ranar Talatar da ta wuce.

A lokacin tsagaita bude wutar na awowi 72, wakilan Isra'ila da na Palasdinawa a birnin Alkhahira sun kasance suna tattaunawa, sai dai ba kai tsaye ba a kan samar da yarjejeniyar tsagaita bude wutar yakin da aka fara a watan Yuli. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China