in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabuwar yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta sa'o'i 72 ta fara aiki a zirin Gaza
2014-08-11 20:27:00 cri
A sanyin safiyar ranar 11 ga wata bisa agogon zirin Gaza, sabuwar yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta sa'o'i 72 ta fara aiki a zirin, wadda kasar Masar ta shiga tsakani.

An kiyasta cewa, wakilan kasashen Palesdinu da Isra'ila za su yi shawarwari a wannan rana a birnin Alkahira, hedkwatar kasar Masar dangane da cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta dogon lokaci.

An labarta cewa, dalilin da ya sa bangarorin 2 suka cimma wannan sabuwar yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta sa'o'i 72 shi ne domin kai wa kayayyakin agaji a zirin na Gaza, tare da gyara gine-ginen da aka lalata a wurin cikin hanzari. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China