in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci kasashen duniya da su matsa wa Isra'ila lambar tsagaita wuta a Gaza
2014-08-04 09:58:13 cri

Shugaban Palesdinawa Mahmoud Abbas ya yi kira ga kasashen duniya da su matasa wa Isra'ila lamba don ta amince da shirin tsagaita bude wuta a Zirin Gaza da kasar Masar ta kira.

Shugaba Abbas wanda ya yi wannan kiran cikin wata sanarwa, ya ce muddin har Isra'ila ta ki amincewa da tsagaita bude wuta, hakika ita za ta dauki alhakin dukkan sakamakon da ya biyo baya na ci gaba da fadan da take y i a zirin Gaza.

Bugu da kari ya ce, Isra'ila tana aikata mummuna laifi kan al'ummar Palesdinawa tare da kai hare-hare kan makarantun da ke karkashin MDD, da lalata gidajen jama'a inda take halaka tare da raunata maza, mata da kuma kananan yara.

Tun a ranar 8 ga watan Yuli ne Isra'ila take kaddamar da hare-hare kan zirin Gaza, inda ta kashe mutane 1,766 tare da jikkata 9,500. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China