Mr. Wang wanda ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin da yake ziyarar aiki a kasar Masar, ya ce kasar Sin na goyon bayan duk wani mataki na shiga tsakanin bangarorin biyu.
Da yake karin haske game da matakan da ya dace a dauka domin kawo karshen dauki ba dadin da ke aukuwa tsakanin sassan biyu, Mr. Wang ya ce da farko, akwai bukatar dukkanin bangarorin su dakatar da musayar wuta, su kuma kare rayukan fararen hula, tare da wanzar da yanayin zaman lafiya a yankinsu.
Na biyu ya ce Sin na goyon bayan duk wani shirin shiga tsakani da Masar, tare da sauran masu ruwa da tsaki za su jagoranta.
Kaza lika a cewarsa Sin na goyon bayan bukatar Falasdinawa ta kafuwar kasa mai 'yanci bisa doka.
Na hudu Mr. Wang ya yi kira ga kwamitin tsaron MDD da ya dauki dukkanin matakan da suka wajaba, don ganin an kawo karshen wannan rikici, tare da warware matsalolin dake haddasa sabani tsakanin sassan.
Daga karshe ministan harkokin wajen kasar ta Sin ya ce ya zama wajibi kasashen duniya su kara maida hankali game da halin da Falasdinawa ke ciki, tare da samar da dukkanin agajin jin kai da ya dace a kan lokaci. (Saminu Hassan)