Liu Jieyi ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin taron babban zauren MDD game da halin da ake ciki a Gaza, inda ya shaidawa taron damuwar Sin game da yawan fararen hulan da suka rasa rayukansu da wadanda ke bukatar agajin jin kai sakamakon fadan da aka kwashe makonni hudu ana yi tsakanin mayakan Hamas da sojojin Isra'ila.
Ya ce, shi ma manzon kasar Sin mai kula da yankin gabas ta Tsakiya, ya ziyarci yankin har sau biyu cikin wata guda don ganin an tsagaita bude wuta tare da hawan teburin tattauna tsakanin Isra'ila da Palesdinu.
Bugu da kari a ranar 3 ga watan Agusta, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya ziyarci kasar Masar da nufin yin musayar ra'ayoyi da shugabannin kasar da kuma babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa a kokarin ganin an tsagaita bude wuta tsakanin sassan biyu, baya ga wani shirin daidaita rikicin da ya gabatar.
Mr Lui ya ce, kasar Sin tana maraba da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta sa'o'i 72 da bangarorin biyu suka amince da ita tare da shiga tattaunawar tsagaita bude wuta na dogon lokaci, matakin da Sin ke fatan zai kai ga cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta mai dorewa nan ba da dadewa ba.
Ya kuma bayyana kudurin Sin na ci gaba da taka muhimmiyar rawa tare da sauran kasashen duniya don kawo karshen rikicin da ke tsakanin Isra'ila da Palasdinu cikin hanzari, da kuma samar da zaman lafiya a yankin gabas ta Tsakiya. (Ibrahim)