Rahotonni sun nuna cewa 'yan kabilar Yezides na ci gaba da kwarara zuwa kan iyakar Turkiya, yayin da wasu rahotannin kuma suka bayyana cewa akwai miliyoyin jama'a dake cikin tsaka mai wuya a yankunan tsaunukan Sinjar dake bukatar taimakon jin kai cikin gaggawa, matsala ce dake ta da hankali kuma ta gaggawa, in ji kakakin Ban Ki-moon a cikin wata sanarwa.
Shugaban MDD ya kira ga gamayyar kasa da kasa musamman ma masu fada a ji da kuma halin da ake ciki ba su damar kawo wani ci gaba mai kyau kan wannan matsala, su tallafawa gwamnati da al'ummar Iraki da kuma yin duk wani kokari wajen ganin an taimaka ga kawo karshen wahalar mutanen da wannan rikici na yanzu ya shafa a Iraki. (Maman Ada)