in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Obama ya ba da umarnin isar da kayayyakin agaji ta sama a Iraki
2014-08-08 11:08:20 cri
Shugaba Obama na Amurka ya bayar da umarnin isar da kayayyakin agaji ta sama a kasar Iraki, ganin yadda yanayin jin kai ke tabarbarewa a kasar.

Shugaba ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a daren Alhamis, inda ya bayar da umarnin daukar matakan kai hari ta sama idan har akwai bukatar yin haka kan mayakan kishin Islama da suka nausa zuwa yankin Kurdawa na kasar ta Iraki inda suka kame madatsar ruwa mai girma ta kasar.

Bugu da kari shugaban ya sanar da cewa, Amurka ta jefo kayan abinci da ruwa ta sama kan wani tsaunin da ke arewacin kasar Iraki a ranar Alhamsi, inda mayakan suka killace wasu kananan kabilu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China