Haka zalika, kasar Sin ta yarda da matakan da aka dauka, wadanda za su amfanawa kokarin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a kasar ta Iraki, muddin dai wanda ya dauki matakan ya girmama mulkin kai na kasar Iraki. Haka kuma kasar Sin ta nuna fatanta na ganin an maido tsari da oda da kwanciyar hankali a kasar tun da wuri.
Kafin haka kuma, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya sanar a daren ranar 7 ga wata cewa, ya ba da umarni ga sojojin kasar don su kai hare-hare ta jiragen saman yaki ga dakarun masu tsatsauran ra'ayi na kasar Iraki, tare da isar da agajin jin kai zuwa ga fararen hulan kasar wadanda suka tsunduma cikin tsaka mai wuya. (Bello Wang)