Sin tana kiran gamayyar kasa da kasa da ta yi aiki yadda ya kamata tare da kuduri mai lamba 2170 dake da manufar karfafa kokari wajen yaki da kungiyoyin ta'addanci, kamar kungiyar kasar musulunci tare Iraki da Levant (ISIS) da kuma kungiyar Al-Nousra (FEN), in ji Liu Jieyi, zaunanen wakilin kasar Sin a MDD bayan an amince da wani kudurin kwamitin tsaro na MDD kan wannan batu da babban rinjaye.
Tun yau da dan lokaci, ISIS da FEN suke ta ci gaba da kai hare hare kan fararen hula, tare da gallazawa jama'a na sauran addinai da kuma al'ummomin wasu kabilu, ta hanyar janyo asarar rayuka daga cikin fararen hula da ba su ji ba su gani ba da kuma ficewar miliyoyin jama'a daga gidajensu, in ji mista Liu, tare da jaddada cewa kungiyoyin kishin Islama sun zamo babbar barazana ga zaman lafiya da tsaron gabas ta tsakiya da ma duniya baki daya.
Manzon Sin ya kira ga gamayyar kasa da kasa da ta bullo da nagartattun matakai domin dakile tallafin makamai, mayaka, da na kudi zuwa ga kungiyoyin ta'addanci domin kawar da yaduwar ta'addanci a kasar Iraki da sauran kasashe, da kuma kokarin tabbatar da zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a yankin gabas ta tsakiya da duniya baki daya.
Kasar Sin, ita ma tana fama da ta'addanci. Muna adawa sosai da ta'addanci ta kowane hali kana kuma za mu ci gaba hadin gwiwa tare da kasa da kasa domin yaki da ta'addanci da kuma hada kokari tare domin murkushe barazanar ta'addanci, in ji mista Liu. (Maman Ada)