Cibiyar bayar da umurni ta Amurka ta bayyana cewa, jiragen saman yakin Amurka sun kai hare-hare 14 kan mayakan da nufin tallafa wa kokarin da ake na kai kayan agaji, kare muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a, ma'aikata da gine-ginen Amurka tare kuma da mara wa dakarun Iraki da na Kurdawa a yakin da suke da 'yan tawayen Iraki da ke kokarin kafa daular musulunci(ISIL).
A ranar Lahadi ne shugaba Obama na Amurka ya sanar da majalisar dokokin kasar cewa, ya bayar da umarni a ranar Alhamis na kai hare-hare a kusa da madatsar ruwar Mosul, don taimaka wa dakarun na Iraki a kokarin da suke na sake kwato madatsar ruwa mafi girma da ke Iraki.
Wannan shi ne umarni na farko da shugaba Obama ya bayar na kai hare-hare ta sama kan kungiyar da ta kwace karin birane da garuruwa yayin da ta ke kara nausa wa Erbil, babban birnin yankin kurdawa mai cin gashin kansa, inda suka yi wa fararen hula da dama ciki har da 'yan kabilar Yazidi marasa rinjaye kofar rago a tsaunin Sinjar.(Ibrahim)