A cewar rahotannin kafofin yada labarai, shi dai Nuri al Maliki, wanda aka zabe shi a matsayin firaministan kasar Iraqi a watan Afilun wannan shekarar ya yanke wannan shawara ce bayan da ya gana da Abadi a wani taro da aka yi, a karkashin shiga tsakanin mataimakin shugaban kasar ta Iraqi Khudhair al-Khuzaie, da tsohon firaministan kasar Ibrahim Ja'afar, wanda kuma jigo ne a jam'iyyar National Alliance ta 'yan mabiya darikar Shi'a.
Tun kafin ya mika kujerar sa ga Abadi, Nuri-al Maliki yana fuskantar matsin lamba, saboda 'yan siyasa sun nuna bukatar samun sabon firaminista wanda zai samu amincewar 'yan kabilar Kurdawa da 'yan Sunni, kuma kasar Amurka da Iran sun jajurce cewa, lokaci ya yi da Nuri-al Maliki zai sauka daga wannan mukami, inda suka lashi takwabin goyon bayan Abadi.
To amma kawo ya yanzu babu wani haske dake nuni da cewar shelar mika mulki a hannun Abadi zai taimaka wajen hada kan dukanin kabilun kasar wadanda ke ci gaba da fuskantar barazanar hare-hare na kungiyar ISIS wacce ta kwace muhimman yankuna guda biyar tun bayan da ta kaddamar da yaki a watan Yunin da ya gabata. (Suwaiba)