Rundunar sojin Kurdawa sun sake kwato garuruwa biyu da kungiya mai kaifin addinin Islam ta IS suka karbe tun da farko a arewacin kasar Iraki a ranar Lahadin nan, sakamakon cigaba da hare-hare ta sama da sojojin Amurka ke kaiwa a kan 'yan kungiyar, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta ruwaito.
Su dai sojojin Kurdawan wato Peshmerga da mayakan yaki da ta'addanci sun hada kansu tare da Jam'iyyar ma'aikata kurdawa ta kasar wajen samun nasarar kwato birnin Makhour ne tare da zama mai cikakken ikon da shi, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta jiwo daga bakin babban kwamandan mayakan yaki da ta'addanci.
Sojojin na Peshmerga sun kuma kwato garin Gwer mai tazarar kilomita 40 daga kudu maso yammacin Arbil babban birnin yankin Kurdawa, bayan da suka samu galaba a kan sojojin 'yan tawaye a safiyar Lahadi, in ji rahoton. Garuruwan Gwer da Makhmor dai kungiyar masu kaifin addini suka kwace shi kwanakin baya, abin da ya kawo babbar barazana ga babban birnin yankin Kurdawa.
Sojojin Amurka dai a ranar Asabar suka ci gaba da kai hare hare har sau hudu ta jiragen sama a kan sojoji 'yan darikar sunni a arewacin kasar, wadanda da farko aka fi sanin su da suna ISIL wato jihohin musulmai na Iraki da levant, kamar yadda sashin tsaron na gwamnatin Amurta ya buga a shafinsa a kan twitter.
Shugaban Amurka Barack Obama tun da farko a ranar Asabar ya ce harin da sojojinsa ke kai wa a Iraki zai dauki lokaci, amma bai ba da karin haske a kan tsarin ayyukan sojojin na shi ba. Yana mai cewa, ba ya zatan za'a iya warware wannan matsala cikin makwanni.
Ya kuma yi gargadin cewa, sabon kudurin samar da tsaro a Iraqi ya kunshi daukar matakan soji da da sauyi a yanayin siyasa, wani aiki ne da zai dauki lokaci mai tsawo, ya dai kara bada tabbacin cewa, kasarsa ba za ta sake tura sojojin kasa zuwa Iraki ba.(Fatimah Jibril)