A cikin wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, Mr. Ban wanda ya yaba ma shugaban kasar ta Iraqi yanzu Fuad Masoum, wanda ya dora alhakin ganin an kafa sabuwar gwamnati a kan Haider al-Abadi. Ya kuma ba da kwarin gwiwwa ga firaministan na Iraqi da ya kafa gwamnati da kowa zai yi amanna da ita da ta kunshi daukacin al'umma da kuma wa'adi yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Tun da farko a wannan ranar sai shugaban kasar na Iraqi Fuad Masoum ya bukaci firaministan shi Haider al-Abadi, mataimakin kakakin majalissar dokokin kasar da kuma dan jam'iyyar Dawa da su kafa sabuwar gwammanati mai kamawa.
Sai dai 'yan siyasa masu goyon bayan tsohon firaminista mai barin gado Nuri al-Maliki a ranar Litinin din har ila yau sun ki amincewa da al-Abadi bisa zargin cewa, ba ya wakilitarsu, don haka ba shi da halarcin yin haka.(Fatimah Jibril)