A wannan rana, sakataren hukumar tsaron kasar Iran Ali Shamkhani ya taya al-Abad murnar nada shi a matsayin sabon firaministan kasar Iraki, kana ya yi kira ga jam'iyyun siyasa daban daban na kasar Iraki da su hada kai don tinkarar barazana daga kasashen waje. Wannan ne karo na farko da kasar Iran ta bayyana ra'ayinta kan nada sabon firaminista a kasar Iraki.
Sarkin kasar Saudiyya Abdullah Bin Abdul-Aziz ya aiko da sakon taya murna ga sabon firaministan kasar Iraki, inda ya ce, yana fatan kasar Iraki za ta mai da hankali wajen hadin kai a tsakanin kungiyoyin addini da kabilu daban daban a matsayin tushen tabbatar da zaman lafiya a kasar a karkashin jagorancin al-Abad. (Zainab)