An ba da labarin cewa, wasu mambobin majalisar ministocin Japan a yau Jumma'a 15 ga wata sun kai ziyara a haikalin Yasukumi, sannan kuma firaminista Shinzo Abe ya mika kudin yin ibada.
A cewar Madam Hua, haikalin Yasukumi ya mara baya ga wadanda suka aikata laifin yaki cikin babban yakin duniya na biyu, tare da yin alfahari da laifufukan da suka yi, yadda shugaban kasar ya mikawa haikalin kudin yin ibada wani abu ne da ya bayyana matsayi na kuskure da gwamnatin Japan ke dauka kan tarihi. Hakan ya sa, Sin ta nuna matukar rashin jin dadi.
Bugu da kari, Madam Hua ta yi nuni da cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Japan na iya samun ci gaba muddin kasar ta daidaita matsayin da ta dauka kan harin da ta kai da yin watsi da ra'ayin karfin soja. (Amina)