Ranar 7 ga watan Yuli, rana ce ta cikon shekaru 77 ta barkewar yakin kin harin Japan da dukkan al'ummar kasar Sin suka yi, a safiyar wannan rana ta Litinin, wakilai daban daban a nan birnin Beijing sun shirya gaggarumin biki a dakin tunawa da yakin kin harin Japan da jama'ar kasar Sin suka yi, inda babban sakataren JKS, shugaban kasar, kuma shugaban kwamitin harkokin sojoji na JKS Mista Xi Jinping ya halarci bikin tare da gabatar da wani muhimmin jawabi. Wasu kwararru na kasashen ketare sun yi nuni da cewa, tunawa da yakin kin harin Japan da kasar Sin take yi bisa matakin koli tana da muhimmiyar ma'ana, kuma tilas ne al'ummun kasashen duniya su yi taka tsantsan ga farfadowar masu tsatsauran ra'ayi na Japan, ta hanyar nuna adawa a tsanake kan farfadowar manufar masu ra'ayin nuna karfin soja na kasar.
Wani kwararre daga cibiyar nazari tarihin arewa maso gabashin Asiya a kasar Korea ta Kudu ya ce, cin nasarar yakin kin harin Japan da kasar Sin ta samu, ba kawai ya haifar da cimma burin samun 'yancin kai ga jama'a ba ne, a'a har ma ya bai wa kasar Sin babbar gudummawa ta samun damar shimfida yanayin zaman lafiya a dukkanin duniya. Hakikanin tarihi dai ba ya canzawa, kuma ba za a iya mantawa da shi ba, al'amuran tarihin wannan yanki sun shafi tsaron Asiya da kuma zaman lafiya da zaman karko a duk fadin duniya.
Shi ma wani kwararren Faransa da ke nazarin harkokin kasar Sin Mista Pierre Picard ya bayyana cewa, dalilan da ya sa kasar Sin ke tunawa da ranar barkewar yakin kin harin Japan bisa babban mataki su ne, ba batu ne na nuna kyama ba, illa dai tunawa da mutane da suka rasa rayukansu, da kiyaye tarihi yadda ya kamata, da yin gargadi domin gaba, da yin kira da kiyaye zaman lafiya. A 'yan kwanakin baya, gwamnatin kasar Japan ta yi kokarin maido da ikon daukar matakan soji domin kiyaye tsaron kawayenta, kuma an girmama wasu fursunonin yaki a kasar, wadannan abubuwa dai sun zama shaidu kan yadda mahukuntan Japan suke watsi da hakikanin tarihi. (Danladi)