in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Obama da Shinzo Abe sun yi shawarwari
2014-04-25 20:47:38 cri

Shugaban kasar Amurka Barack Obama, wanda yake ziyara a kasar Japan, ya yi shawarwari da firaministan kasar Japan Shinzo Abe a birnin Tokyo a ran 24 ga wata da safe.

A shawarwarin da suka yi, bangarorin biyu sun yi musanyar ra'ayoyinsu dangane da inganta kawancen Japan da Amurka, da kuma duba ci gaba da aka samu a gun shawarwari a tsakanin kasashen biyu kan yarjejeniyar hadin gwiwar kasashen da ke kewayen tekun Pacific wato TPP, da halin da ake ciki shiyyar da dai sauransu. Game da burin Shinzo Abe na sassauta ikon kare kanta da aka kayyade ta, an yi hasashen cewa, mai yiyuwa ne Obama zai yi maraba da nuna goyon baya kan batun. Ban da wannan kuma, bisa labarin da muka samu daga gidan talibijin na NHK na Japan, an ce, sakamakon karuwar matakan da kasar Sin ta dauka a kan teku, mai yiyuwa ne kasashen biyu za su jaddada batun 'yancin zirga-zirga a yankin sararin sama da na teku, da amincewa da wai 'tsibirin Diaoyu na karkashin mulkin Japan ne, wanda ya dace da yarjejeniyar tabbatar da tsaron juna na Japan da Amurka'. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China