in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gamayyar kasa da kasa ta yi suka ga wasu jami'an Japan da kai ziyarar ban girma a haikalin Yasukuni
2013-08-16 15:30:08 cri
Gamayyar kasa da kasa ta yi suka mai tsanani ga wasu jami'an gwamnatin kasar Japan dangane da ziyarar ban girma da suka kai ga wadanda suka aikata laifuffuka a yakin duniya na biyu a haikalin Yasukuni ran 15 ga wata. Harkokin da masu tsattsauren ra'ayin kasar Japan suka yi wajen yi musu ziyara da kuma gyara tarihin kasar ba kawai sun bata ran jama'ar kasashe masu makwabtaka da kasar ba ne, domin kuwa lamarin ya bata ran duk jama'ar da aka yi musu laifuffuka da kuma kasashen da suka shiga yakin duniya na biyu.

Kamfanin dillancin labaran kasar Burtaniya BBC ya bayyana cewa, duk ziyarar ban girma da jami'an kasar Japan suka kai a haikalin Yasukuni ya nuna kin yarda kan laifuffukan da kasar ta yi ga kasashen Sin, Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu da dai sauran kasashe makwabtanta.

Ran 15 ga wata, ta shafin intanet dinsa, kamfanin dillancin labaran Ansa na kasar Italiya ya ba da labarin, inda ya nuna cewa, tun lokacin da Shinzo Abe ya kama aiki a matsayin firaministan kasar Japan, ya ki amince da laifuffukan da kasarsa ta yi lokacin yakin duniya na biyu, kuma bai nuna alamun rokon gafara ko kadan ga jama'ar kasashe masu makwabtaka da kasar ba.

Kuma bisa labarin da jaridar duniyar matasa ta kasar Jamus ta bayar, an ce, ran 14 ga wata, cikin wata wasika da kungiyar 'yan matan kasar Japan da ke birnin Berlin ta aika wa Shinzo Abe, ta yi kira ga gwamnatin kasar da ta yi rokon gafara da kuma biyan diyya ga matan da sojojin kasar Japan suka tilasta musu domin aikin karuwai a yayin yakin duniya.

A sa'i daya kuma, ran 15 ga wata, kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ya ba da sharhi, inda ya bayyana cewa, ya kamata kasashen duniya su hada kai domin hana gwamnatin Japan ta cigaba da daukan matakan da ba su dace ba, kuma masu tsattsauren ra'ayin gwamnatin kasar Japan sun ki amincewa da laifuffukan da kasar ta yi yayin yakin duniya na biyu, har sun mai da wadanda suka shiga yakin a matsayin jaruman kasa, lamarin da ya nuna mana cewa, suna son yin musu da kuma gyara tarihin yakin yadda bai cancanta ba. Shi ya sa, ya kamata gamayyar kasa da kasa su hada kai don yin kira ga kasar Japan da ta girmama tarihi da kuma dakatar da gwamnatin kasar dangane da gyara tsarin mulkin domin zaman lafiya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China