in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyya mai mulki a Japan ta samu kaso mai yawa a sakamakon zaben majalissar dokoki
2013-07-22 11:04:56 cri
Rahotanni daga kasar Japan na nuna cewa jam'iyyar mai mulkin kasar, da jam'iyyar LDP, da kuma sabuwar jam'iyyar Komeito ne suka lashe kujeru mafiya yawa, bayan kammalar zaben 'yan majalissun dokokin kasar, wanda aka sanar da sakamakonsa ranar Lahadi 21 ga wata. Wannan dai mataki ya kawo karshen rarrabuwar kai, tare da share fagen bunkasar tattalin arzikin kasar da tuni jam'iyyun suka ayyana baiwa cikakkiyar kulawa.

Jam'iyyar dake mulkin kasar dai ta yi gaba da kujerun majalissun dattijai 76, yayin da LDP da samun kujeru 65, sai kuma sabuwar jam'iyyar Komeito da ta tsira da kujeru 11.

Bisa jimilla jam'iyyar dake mulkin kasar ta samu kujerun da yawansu ya kai 135, cikin daukacin kujerun majalissar dattijai 242. Har ila yau jam'iyya mai mulkin ce ke da rinjayen kujerun wakilci a majalisar wakilai mai matukar tasiri, lamarin da ke nuni ga irin rinjayen da jam'iyyar ke da shi a zaurukan majalissun biyu.

Da yake jawabi yayin wani taron 'yan jaridu, firaministan kasar kuma jagoran jam'iyyar LDP Shinzo Abe, ya yi alkawarin daukar dukkanin matakan da suka wajaba, domin kara habaka tattalin arzikin kasar cikin sauri, tare da samar da daidaito a fagen siyasa, musamman ganin acewarsa, yanzu haka an kawo karshen rarrabuwar kai da ke barazana ga kyakkyawan yanayin siyasar kasar. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China