Ziyarar da Shinzo Abe ya kai a wurin ibada Yasukuni, kalubalantar dokar kasa da kasa bayan yakin duniya na biyu ce
A ranar 8 ga wata, a birnin New York, hedkwatar M.D.D., zaunannen wakilin kasar Sin a M.D.D. Liu Jieyi ya bayyana cewa, ziyarar da firaministan Japan Shinzo Abe ya kai a wurin ibada Yasukuni tamkar kalubalantar dokokin kasa da kasa bayan yakin duniya na biyu ce wadda ke karkashin inuwar kundin tsarin mulki na M.D.D.
A wannan rana, Mr Liu Jieyi ya shaidawa kafofin yada labaru na duniya da ke M.D.D. game da batun.
Mr. Liu ya ce, ya kamata kasashen duniya su yi hattara tare da jan kunnen Shinzo Abe cewa, dole ne ya gyara kuskuren sa. Kamata ya yi kasashen duniya su dukufa ka'in da na'in wajen kiyaye kundin tsarin mulki na M.D.D., don hana ko wane mutum maida hannun agogon baya, da magance kasarsu shiga turba mai hadari.(Bako)