A cikin shirye-shiryen da aka gabatar, an ce, ziyarar da shugabannin Japan suka kai a wurin ibadar Yasukuni da aka takaddama a kai, wani batu ne da ke da muhimmanci ga makomar raya kasar, kuma babban batu na masu tsattsauran ra'ayi shi ne zaman lafiya ko yaki, shimfida adalci ko kulla mugun nufi, haske ko duhu.
Ya ce, idan kasar Japan ba ta daina irin wannan mummunan tunani ba, ba za a kawar da yiwuwar wani yakin duniya ba. Kasar Sin tana fatan warware batun ta hanyar zaman lafiya, amma Sin za ta kimtsawa duk wani abin da ka iya biyo baya, kasar Sin tana fatan kasashen duniya za su hana tunanin dawo da wani nau'in mulkin mallakar duniya ta hanyar soji na kasar Japan. (Bako)