Gwamnatin kasar ta Japan ta gudanar da wani taron gaggawa da yammacin jiya Talata, domin zartas da wasu kudurorin da suka shafi kyautata bayanai kan tsarin mulkin kasa, da maido da ikon daukar matakan soji domin kiyaye tsaron kawayenta.
Sai dai jim kadan da aukuwar hakan, bangarori daban-daban na al'ummar kasar ta Japan sun bayyana rashin jin dadin su, da kin yarda da wadannan kudurori, tare da bukatar Shinzo Abe da ya yi watsi da kudurorin.
Kungiyar manema labaru ta kasar Japan ta ba da wata sanarwa a wannan rana, dake cewa aiwatar da wannan iko zai jefa Japan cikin yaki. Kungiyar ta kuma yi fatan al'ummar kasar za su nuna matukar kiyayya ga matakan da gwamanatin ta Shinzo Abe take dauka.
A hannu guda kuma, masanan a fannonin ilmi, da doka, da shari'a da gwamnonin sassa daban-daban, sun yi Allah wadai da wadannan kudurorin da Shinzo Abe ya zartas, wadanda suka sabawa burin jama'ar kasar. (Amina)