An labarta cewa, a daren ranar 13 ga wata, kasashen Palesdinu da Isra'ila sun amince da tsawaita wa'adin tsagaita bude wuta a zirin Gaza zuwa kwanaki 5, wanda zai cika nan ba da dadewa ba, don haka bangarorin 2 za su ci gaba da shawarwarin da suke kan tsagaita bude wuta cikin dogon lokaci a birnin Alhakira, hedkwatar kasar Masar.
Dangane da hakan, Madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, yanzu haka Palesdinu da Isra'ila suna shawarwari a Alkahira. Kasar Sin ta yi kira da su kai zuciya nesa a yayin da suke tsagaita bude wuta, su gaggauta yin shawarwarin yadda ya kamata, a kokarin cimma wata yarjejeniyar tsagaita bude wuta na dogon lokaci. (Tasallah)