Mr. Ban ya kuma yi kira da a rungumi matakan gudanar da shawarwari, wajen warware rikicin kasar ta Ukraine.
Mr. Ban ya bayyana cewa, ci gaba da tashe-tashen hankula a yankin gabashin kasar Ukraine, ya haddasa karin salwantar rayuka da jikkatar mutane, baya ga tabarbarewar yanayin jin kai a fadin kasar baki daya, lamarin da ke nuna matukar bukata kawo karshen rikicin kasar ba tare da wani bata lokaci ba.
Har wa yau Mr. Ban wanda ya bayyana bukatar warware matsalar kasar ta hanyar shawarwari, ya kuma kara da cewa, ya zuwa yanzu ba a cimma wata nasara ba, a kokarin da ake yi ta fannin diflomasiya.
Don haka a cewarsa kamata ya yi bangarorin da wannan rikici ya shafa, su yi kokarin aiwatar da shawarwarin da aka cimma kan batun kasar ta Ukraine, tsakanin wakilan kasashen Amurka, da Rasha, da Ukraine da kuma kungiyar EU.
A ranar Asabar ne dai dakaru masu adawa da gwamnatin kasar ta Ukraine, suka harbo jirgin saman sojin kasar, a wani wuri dake kusa da filin jirgin saman Luhansk, lamarin da ya sabbaba mutuwar daukacin mutane 49 dake cikinsa. (Maryam)