A jiya Jumma'a ma ministan harkokin cikin gidan kasar ta Ukraine ya bayyana cewa, sojojin kasar sun kai wani farmaki kan dakaru masu adawa da gwamnati, suka kuma kwace yankin Mariupol, tare da mamaye dukkanin sansanonin dakarun.
A hannu guda kuma, yayin tattaunawar da suka yi ta wayar tarho, shugaba Vladimir Putin na Rasha, ya shaidawa shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Turai José Barroso cewa, ya zama wajibi Ukraine ta dakatar da ayyukan soji a gabashin Kasar ta.
Har ila yau wasu rahotanni na cewa, mahukuntan Rasha da na kungiyar EU sun amince ministocinsu da masana su shawarta da takwarorinsu na Ukraine, kan batun daddale yarjejeniyar mu'amala tsakanin Turai da Ukraine. (fatima)