in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Rasha da Ukraine sun yi shawarwari kan yanayin gabashin Ukraine ta wayar tarho
2014-06-13 16:09:41 cri
Sakataren shugaban kasar Rasha a fannin watsa labarai Dmitri Peskov, ya bayyana a ran 12 ga wata cewa, shugaban kasar Vladimir Putin ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Ukraine Peter Poroshenko ta wayar tarho, inda suka tattauna kan shirin sassauta yanayin gabashin kasar Ukraine, sa'an nan, sun yi shawarwari kan raya dangantakar kasashen biyu.

A nasa bangaren, ofishin kula da ayyukan watsa labarai na shugaban kasar Ukraine, ya sanar da cewa, yayin tattaunawar shugabannin kasashen biyu, shugaba Poroshenko ya bayyana cewa, ko kadan ba zai amince, tankokin yakin kasar Rasha su ratsa iyakarta a hanyarsu ta shiga Ukraine ba.

Wannan shi ne karo na biyu da shugabannin kasashen biyu suka yi cudanya da juna, baya ga ganawarsu a gun bikin taya murnar cikon shekaru 70 da kwace Normandy da aka yi a makon jiya, inda shugabannin suka kwashe mintoci 15 wajen tattauna kan yadda za a iya sassauta halin da kasar Ukraine ke ciki. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China