in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya tattauna da ministocin kasar Masar kan batun cinikayya
2014-08-03 16:51:53 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya fara ziyarar aikinsa a kasar Masar a jiya Asabar, inda ya tattauna da ministocin kasar daban-daban, karkashin jagorancin ministan harkokin wajen Masar Sameh Shukri.

Cikin jami'an da ya zanta da su dai hadda ministan masana'antu da cinikayya Mounir Fakhry Abdel Nour, da ministan wutar lantarki da makamashi Sabah Mohammed Shakir, da minista mai kula da zuba jari Ashraf Salman.

Sauran jami'an sun hada da wakilin ministan harkokin sufuri, da kuma shugaban hukuma mai kula da harkokin kogin Suez Mohab Memish, da ministan hadin kan kasa da kasa, inda suka tattauna kwarai kan yadda bangarorin biyu za su habaka hadin kai tsakaninsu.

Mr Wang ya bayyana cewa, ziyarar ta sa ta wannan karo na da nufin bayyana matsayin Sin, game da goyon bayan tursasa sauyin jagoranci a kasar, tare kuma da nuna kyakkyawan fata ga bunkasuwar kasar ta Masar, matakin da ya nuna muhimmancin da Sin ke dora kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

A wani ci gaban kuma, Wang Yi ya ce shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawara a gun taron ministoci, na dandalin tattauna hadin kai tsakanin Sin da kasashen Larabawa, wadda ta shafi raya sabuwar hanyar silik a kasa, da bangaren teku a shekarar nan ta 2014. Ban da hakan, Wang ya tabo batun ziyarar da firaminista Li Keqiang ya gudanar a nahiyar Afrika, inda ya gabatar da shawarar hadin kai tsakanin Sin da nahiyar, wajen gina manyan ababen more rayuwa.

Ya ce Masar tana wani muhimmin wuri, a mahadar sabuwar hanyar silik a kasa da kuma teku, lamarin da ya ba ta matsayi na musamman.

Kazalika, ministan na Sin ya ce tsarin da kasashen biyu ke bi wajen raya kan su ya yi kama da juna. Kana Masar na samun daidaito a fannin siyasa, tare da bunkasa yadda ya kamata, ya yin da Sin ke fatan kara hadin gwiwa da ita a dukkan fannoni. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China