Mahlab wanda ya yi aiki na tsawon watanni biyar a matsayin firaministan rikon kwaryar kasar zai ci gaba da rike wannan mukami, bayan da Al-Sisi ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar.
Sabuwar majalisar dai tana kunshe ne da ministoci 34, 13 daga cikinsu sabbi ne sai kuma mata 4 kacal.
An kuma nada Ashraf Salman a matsayin sabon ministan kula da harkokin zuba jari, da tsohon jakadan kasar Masar a kasar Amurka Sameh Shukri wanda aka nada a matsayin sabon ministan harkokin waje. (Ibrahim)