Rahotanni daga kamfanin dillancin labaran kasar Masar MENA, sun ce ya yi ganawar tasu a jiya Asabar, Sisi da Mr. Blair sun tattauna kan mummunan yanayin da aka shiga, tun bayan da Isra'ila ta fara luguden wuta kan yankunan zirin Gaza a Talatar da ta gabata, lamarin da ya yi sanadiyar rasuwar mutane 127, baya ga kimanin mutane dubu daya da suka jikkata.
Mr. Blair da shugaba Sisi dai sun yi kira ga bangaorin biyu da su kai zuciya nesa, su dakatar da kaiwa juna farmaki, tare da komawa teburin shawara, domin kaucewa karuwar asarar rayukan fararen hula.
A wani ci gaban kuma, kasar Masar ta bude kan iyakarta da Gaza, domin baiwa wadanda suka samu raunuka damar samun jiyya a asibitocinta, yayin da a hannu guda kuma ta aike da tan 500 na kayan abinci da magunguna ga yankunan da suke cikin tsananin bukata.
A ranar Jumma'ar da ta gabata ma dai Masar ta bayyana rashin jin dadin ta, ga abin da ta kira daukar matakin soji, da amfani da karfin tuwo da ya wuce kima, kan yankunan Falasdinawa. (Saminu Alhassan)