Ma'aikatar harkokin wajen kasar Masar ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, an yanke wannan shawara ce ganin yadda kasar ta gudanar da kuri'ar raba gardama kan kundin tsarin mulkin kasar da zabe da kuma rantsar da sabon shugaban kasar da aka gudanar.
A ranar Talata ne kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar ya yanke shawarar sake dawo da kasar cikin harkokin kungiyar, bayan da aka dakatar da ita a watan Yulin da ya gabata, sakamakon hambarar da zababben shugaban kasar Mohamed Morsi da sojojin kasar suka yi biyo bayan wani boren gama gari da aka yi game da mulkinsa na shekara guda kacal. (Ibrahim)