in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Har yanzu ba a gano inda 'yan matan Chibok 219 suke ba
2014-06-22 17:30:08 cri

Rahotanni daga tarayyar Najeriya na nuna cewa kawo yanzu akwai 'yan mata 276 219 da dakarun kungiyar Boko Haram ke tsare da su, sama da watanni 2 da sace 'yan mata 276 daga makarantar garin Chibok a jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya.

Hakan dai na kunshe ne cikin rahoton kwamitin bincike da shugaban kasar Goodluck Jonathan ya kafa, domin tantance wannan batu yadda ya kamata.

Rahoton wanda jagoran kwamitin binciken Ibrahim Sabo ya gabatarwa shugaba Jonathan, ya nuna cewa 'yan mata 276 ne dakarun kungiyar ta Boko Haram suka sace, inda 57 daga cikin su suka samu kubuta, lamarin da ya nuna cewa har ya zuwa yanzu akwai ragowar 219 dake hannun dakarun kungiyar.

Sabo ya ce, kwamitin na sa ya ziyarci garin Chibok a ran 29 ga watan Mayun daya gabata, ya kuma tuntubi shugabannin al'ummar yankin, tare da zantawa da iyalan 'yan mata hudu da suka samu kubuta daga hannun dakarun.

Da yake tsokaci jim kadan da karbar kundin rahoton binciken, shugaba Jonathan ya bayyana matukar bakin ciki game da halin da ake ciki, tare da alkawarta daukar dukkanin matakan da suka wajaba domin yakar ayyukan ta'addanci.

Shugaban Nijeriyar ya kara da cewa gwamnatin kasar mai ci, ba zata kyale kungiyar ta Boko Haram, ta ci gaba da cin karenta ba babbaka ba. Jonathan ya kuma yi kira ga daukacin 'yan Nijeriya, musamman ma jami'an dake lura da makaratun yankunan arewa maso gabashin kasar, da su tabbatar da sun bada kariya ga dalibai yadda ya kamata. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China