in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tsige shugaban hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya daga mukaminsa
2013-03-12 19:41:43 cri
A ranar Litinin ne shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya bayar da umarnin tsige Harold Demuren, babban darektan hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman kasar(NCAA) daga mukaminsa.

Sanarwar da shugaban na Najeriya ya bayar a ranar Talata wadda ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya, ta ce, tsige shugaban hukumar ya fara aiki nan take daga ranar Talata, amma har yanzu ba a nada wanda zai maye gurbin nasa ba.

Tsige Demuren ya biyo bayan nazarin da aka yi dangane da rashin daukar matakan da suka dace kan abubuwa da dama da suka shafi masu ruwa da tsaki a bangaren zirga-zirgar jiragen sama. Sanarwar ta ce shugaban na Najeriya ya yi masa fatan alheri a aikinsa na gaba.

Kafin wannan sanarwa ta ranar Talata game da tsige shi, ana ganin dama Demuren ya kusa rasa aikinsa, sakamakon mummunan hadarin jirgen saman da ya yi sanadiyar rayukan mutane 163 a ranar 3 ga watan Yuni na shekara ta 2012 wanda ya faru a jihar Lagos da ke kudu masu yammacin kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China