Mista Kenyatta ya nuna yabo a ranar Jumma'a da yamma kan ci gaban dangantaka tsakanin kasashen biyu, wanda a cewarsa yake bude wani muhimmin babi. Fitar da kayayyakin kasar Kenya zuwa kasar Najeriya ya fado kan dalar Amurka miliyan 33 a shekarar 2012 kasa ga dalar Amurka miliyan 37 a shekarar 2008, a yayin da kuma shigo daga kayayyaki daga tarayyar Najeriya suka ragu da dalar Amurka dubu 550 kasa da dalar Amurka miliyan 1,85, a cewar wasu alkaluman hukumar kididdiga ta kasar Kenya.
Shugabannin biyu sun dauki niyyar kara karfafa musanyar kasuwanci tsakanin kasashen biyu, da kuma bunkasa kasuwanci tsakanin kasashen Afrika da kuma fadada hanyoyin kara zuba jari. Haka zalika shugabannin kasashen biyu sun yi kira ga hukumomin da abun ya shafa na kasashen biyu ga daukar matakan da suka wajaba na rage shingayen haraji da na wadanda ba su shafi kasuwancin ba tsakanin kasashen biyu. (Maman Ada)