in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe mutane da dama lokacin arangama tsakanin sojoji da 'yan boko haram
2013-05-18 17:13:05 cri
A jihar Katsina dake arewacin Nigeriya mutane da dama sun mutu a wani arangama daya faru a tsakanin 'yan kungiyar nan ta Boko Haram da kuma jami'an soji a daren Alhamis,kamar yadda jami'an tsaron suka sanar a ranar jumma'a.Kuma wadanda suka mutu sun hada da sojoji 3 da wadansu 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram da yanzu haka suka fi samun asarar 'ya'yan su tun daga shekarar ta 2009.

A ranar Alhamis din ne Sojoji suka sanar da cewar wassu gungun 'yan boko haran sun shiga garin na Daura a jihar Katsina wadda itace mahaifar tsohon Shugaban kasar Nigeriya kuma dan jam'iiyar adawa,Janar Muhammadu Buhari,a cewar Kakakin rundunar sojin Manjo Janar Garba Wahab nan take Sojoji da 'yan sanda suka yi ma wurare uku a garin kawanya suka fara bincikie gida gida domin zakulo wadannan bata gari wadanda aka ji ma rauni kuma ake kyautata zaton sun tsere sun shige gidajen wadansu a garin domin neman mafaka.

Haka kuma inji Jami'in Sojin yace sun shirya hadin gwiwwa wajen wannan aiki tare da jami'an tsaron kasar Nijar domin a yadda bayanai ya nuna kusan kashi 80-90 a cikin 100 na 'yan kungiyar da suka kai wannan hari ba 'yan kasar Nigeriya ba ne,ya yi bayanin cewa 'yan ta'addan sun kai hari a bankuna 4 suka kwashe kudade masu dimbin yawa sai dai motar da suka yi satar da ita an kama ta tare da samun kudaden har ma da manyan bindigogi kiran AK 47 guda 4.

Janar Wahab ya kara da cewa wannan samame da ake yi domin zakulo wadannan miyagu har yanzu yana nan don haka ya shawarci mazauna garin na Daura da kananan hukumomi kamar su Baure,Sandamu,Mashi da Dutsi su ba da hadin kai ga jami'an tsaro domin cimma nasarar aikin su kuma su ba da rahoton duk wani kai komo na wadanda ba su amince da su ba.

Haka kuma Janar Wahab ya shawarci manema labarai da su ba da cikakken goyon bayan su ga jami'an tsaro wajen wannan aiki yana mai cewa wannan nauyi ne da ya rataya a wuyan kowane dan Nigeriya na tabbatar da an samu zaman lafiya mai dorewa a kasar. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China