Gwamnatin tarayyar Nigeria ta bayyana aniyarta, ta ci gaba da daukar matakan ceto mutanen nan 'yan kasashen waje su 8, da wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a arewacin kasar.
Ministan harkokin wajen kasar Olugbenga Ashiru ne ya bayyana hakan, yayin zantawarsa da takwaransa na Faransa Laurent Fabius, a ranar Asabar 16 ga watan nan. Ashiru ya kara da cewa, burin mahukuntan kasar ne ceto mutanen lami-lafiya, ba kuma tare da biyan diyya ba, domin acewarsa baiwa masu garkuwa da mutane kudi ya sabawa dokar kasar.
Ministan ya kara da cewa, Nigeria na iya zamowa sansanin 'yan tada kayar baya a nan gaba, in bacin kokarin da kasar Faransa, da kungiyar ECOWAS ke yi, na fatattakar 'yan tawaye a kasar Mali.
Yayin zantawarsa da manema labaru, Ashiru ya bayyana cewa, tattaunawarsa da takwaransa na Faransa, zai baiwa kasashen biyu damar sake nazartar yanayin dangantakar dake tsakaninsu.(Saminu)